Categories
FAR

FAR 1

Allah ya Halicci Duniya ya kuma Halicci Mutum

1 A sa’ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya,

2 duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen.

3 Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance.

4 Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu,

5 ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.

6 Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.”

7 Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance.

8 Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.

9 Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance.

10 Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau.

11 Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da ‘ya’ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da ‘ya’ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

12 Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da ‘ya’ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau.

13 Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.

14 Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai.

15 Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance.

16 Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin.

17 Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya,

18 su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

19 Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.

20 Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.”

21 Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

22 Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.”

23 Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.

24 Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.”

25 Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

26 Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.”

27 Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su.

28 Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.”

29 Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itacen da yake da ƙwaya cikin ‘ya’yansa su zama abincinku.

30 Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabbar da take duniya, da kowane irin tsuntsun da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance.

31 Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

Categories
FAR

FAR 2

1 Da haka aka gama yin sama da duniya, da rundunansu.

2 A kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa wanda ya yi. Ya kuwa huta a kan kwana na bakwai daga dukan aikinsa da ya yi.

3 Domin haka Allah ya sa wa kwana na bakwai albarka, ya tsarkake shi, don a cikinsa Allah ya huta daga dukan aikin da ya yi na halitta.

4 Waɗannan su ne asalin sama da duniya sa’ad da aka halicce su.

A ranar da Ubangiji Allah ya yi duniya da sama,

5 a sa’an nan ba tsire-tsiren saura a duniya, ƙananan ganyayen saura kuma ba su riga sun tsiro ba, gama Ubangiji Allah bai sa a yi ruwa bisa duniya ba tukuna. A lokacin kuwa babu wani wanda zai noma ƙasar,

6 amma sai ƙāsashi yake tasowa daga ƙasa ya shayar da fuskar ƙasa duka.

7 Sa’an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.

Gonar Aidan

8 Ubangiji Allah kuwa ya dasa gona a Aidan, wajen gabas, a can ya sa mutumin da ya siffata.

9 Ubangiji Allah ya sa kowane itace mai kyan gani, mai amfani domin abinci, ya tsiro, itacen rai kuwa yana tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.(Far 3.22,24; W. Yah 2.7; 22.2,14,19; Eze 47.12

10 Wani kogi kuma ya malalo daga Aidan ya shayar da gonar, daga nan kuwa ya rarrabu ya zama kogi huɗu.

11 Sunan na fari Fishon, shi ne yake malala kewaye da dukan ƙasar Hawila, inda akwai zinariya.

12 Zinariyar ƙasan nan kuwa kyakkyawa ce. Akwai kuma duwatsu masu daraja a wurin.

13 Sunan kogi na biyu Gihon, shi ne wanda yake malala kewaye da ƙasar Kush.

14 Sunan kogi na uku Taigiris ne, wanda yake malala gabashin Assuriya. Kogi na huɗu kuwa Yufiretis ne.

15 Ubangiji Allah ya ɗauki mutumin ya zaunar da shi cikin gonar Aidan ya noma ta, ya kiyaye ta.

16 Ubangiji Allah ya yi wa mutumin umarni, ya ce, “Kana da ‘yanci ka ci daga kowane itace da yake a gonar,

17 amma daga itacen sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci shi za ka mutu lalle.”

18 Sa’an nan sai Ubangiji Allah ya ce, “Bai kyautu mutumin ya zauna shi kaɗai ba, zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”

19 Haka nan fa, daga cikin ƙasar, Ubangiji ya siffata kowace dabba ta cikin saura da kowane tsuntu na sararin sama, ya kawo su wurin mutumin, ya ga yadda zai kiraye su, duk abin da mutumin ya kirayi mai ran kuwa, sunansa ke nan.

20 Mutumin ya bai wa dabbobi duka suna, da tsuntsayen sararin sama, da kowace irin dabba da take cikin saura, amma ba a sami mataimaki wanda ya dace da mutumin ba.

21 Sai Ubangiji Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin. Lokacin da yake barci Ubangiji Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya cike wurin da nama,

22 haƙarƙarin nan kuwa da Ubangiji Allah ya cire daga mutumin ya yi mace da shi, ya kuwa kawo ta ga mutumin.

23 Sai mutumin ya ce, “Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana, za a kira ta mace, don daga cikin mutum aka ciro ta.”

24 Domin haka mutum yakan rabu da mahaifinsa da mahaifiyarsa ya kuwa manne wa matarsa, sun zama ɗaya.

25 Da mutumin da matarsa dukansu biyu a tsiraice suke, ba su kuwa ji kunya ba.

Categories
FAR

FAR 3

Faɗuwar Mutum

1 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”

2 Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar,

3 amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin ‘ya’yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ”

4 Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba.

5 Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”

6 Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, ‘ya’yansa kuma kyawawa, abin sha’awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga ‘ya’yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.

7 Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa’an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.

8 Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la’asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar.

9 Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”

10 Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”

11 Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”

12 Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni ‘ya’yan itacen, na kuwa ci.”

13 Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?”

Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”

14 Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la’ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka.

15 Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”

16 Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi ‘ya’ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”

17 Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga ‘ya’yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la’antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.

18 “Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar.

19 Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.”2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M. Had 12.7)

20 Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa’u, domin ita ce uwar ‘yan adam.

21 Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.

An Fitar da Adamu da Hawwa’u daga Gonar

22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.”

23 Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.

24 Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko’ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.

Categories
FAR

FAR 4

Kayinu da Habila

1 Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.”

2 Ta kuma haifi ɗan’uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne.

3 Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona.

4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin ‘ya’yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa,

5 amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.

6 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi?

7 In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”

8 Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan’uwansa Habila, har ya kashe shi.

9 Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan’uwanka?”

Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan’uwana ne?”

10 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan’uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa.

11 Yanzu fa, kai la’ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan’uwanka daga hannunka.

12 In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”

13 Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina.

14 Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”

15 Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.

16 Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.

Zuriyar Kayinu

17 Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu.

18 An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek.

19 Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai.

20 Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi.

21 Sunan ɗan’uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa.

22 Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan ‘yar’uwar Tubalkayinu Na’ama ne.

23 Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni.

24 Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba’in da bakwai.”

Zuriyar Shitu

25 Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.”

26 Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.

Categories
FAR

FAR 5

Zuriyar Adamu

1 Wannan shi ne littafin asalin Adamu. A sa’ad da Allah ya halicci mutum, ya yi shi cikin siffar Allah.

2 Namiji da ta mace ya halicce su, ya sa musu albarka, ya sa musu suna, Mutum, sa’ad da aka halicce su.

3 Da Adamu ya yi shekara ɗari da talatin, ya haifi ɗa cikin kamanninsa da cikin siffarsa, ya kuwa sa masa suna Shitu.

4 Bayan da Adamu ya haifi ɗansa Shitu, ya yi shekara ɗari takwas, sa’an nan ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

5 Haka nan kuwa dukan kwanakin Adamu shekara ce ɗari tara da talatin, ya rasu.

6 Da Shitu ya yi shekara ɗari da biyar, ya haifi Enosh.

7 Bayan da Shitu ya haifi Enosh ya rayu shekara ɗari takwas da bakwai, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

8 Haka nan kuwa dukan kwanakin Shitu shekara ce ɗari tara da goma sha biyu, ya rasu.

9 Da Enosh ya yi shekara tasa’in, ya haifi Kenan.

10 Bayan Enosh ya haifi Kenan ya rayu shekara ɗari takwas da goma sha biyar, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

11 Haka nan kuwa dukan kwanakin Enosh shekara ce ɗari tara da biyar, ya rasu.

12 Sa’ad da Kenan ya yi shekara saba’in, ya haifi Mahalalel.

13 Bayan da Kenan ya haifi Mahalalel ya yi shekara ɗari takwas da arba’in, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

14 Haka nan kuwa dukan kwanakin Kenan shekara ce ɗari tara da goma, ya rasu.

15 Sa’ad da Mahalalel ya yi shekara sittin da biyar ya haifi Yared.

16 Bayan da Mahalalel ya haifi Yared, ya yi shekara ɗari takwas da talatin, ya kuma haifi ‘ya’ya mata da maza.

17 Haka nan kuwa dukan kwanakin Mahalalel shekara ce ɗari takwas da tasa’in da biyar, ya rasu.

18 Sa’ad da Yared ya yi shekara ɗari da sittin da biyu, ya haifi Anuhu.

19 Bayan da Yared ya haifi Anuhu ya yi shekara ɗari takwas ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

20 Haka nan kuwa dukan kwanakin Yared shekara ce ɗari tara da sittin da biyu, ya rasu.

21 Sa’ad da Anuhu ya yi shekara sittin da biyar, ya haifi Metusela.

22 Bayan da Anuhu ya haifi Metusela, ya yi tafiya tare da Allah shekara ɗari uku ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

23 Haka nan kuwa dukan kwanakin Anuhu shekara ce ɗari uku da sittin da biyar.

24 Anuhu ya yi tafiya tare da Allah, Allah kuwa ya ɗauke shi, ba a ƙara ganinsa ba.

25 Sa’ad da Metusela ya yi shekara ɗari da tamanin da bakwai, ya haifi Lamek.

26 Bayan da Metusela ya haifi Lamek ya yi shekara ɗari bakwai da tamanin da biyu, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

27 Haka nan kuwa dukan kwanakin Metusela shekara ce ɗari tara da sittin da tara, ya rasu.

28 Sa’ad da Lamek ya yi shekara ɗari da tamanin da biyu, ya haifi ɗa,

29 ya sa masa suna Nuhu, yana cewa, “Daga gare shi za mu sami sauƙin aikinmu da wahalar hannuwanmu a ƙasar da Ubangiji ya la’anta.”

30 Bayan da Lamek ya haifi Nuhu ya yi shekara ɗari biyar da tasa’in da biyar, ya haifi ‘ya’ya mata da maza.

31 Haka nan kuwa dukan kwanakin Lamek shekara ce ɗari bakwai da saba’in da bakwai, ya rasu.

32 Sa’ad da Nuhu ya yi shekara ɗari biyar, ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.

Categories
FAR

FAR 6

Muguntar ‘Yan Adam

1 Da mutane suka fara yawaita a duniya suka kuwa haifi ‘ya’ya mata,

2 sai ‘ya’yan Allah suka ga ‘yan matan mutane kyawawa ne, suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura.

3 Sai Ubangiji ya ce, “Numfashina ba zai zauna cikin mutum har abada ba, gama shi mai mutuwa ne. Nan gaba kwanakinsa ba zai ɗara shekara ɗari da ashirin ba.”

4 A waɗannan kwanaki kuwa, ‘ya’yan Allah suka shiga wurin ‘yan matan mutane, suka kuwa haifa musu ‘ya’ya. Su ne manya manyan mutanen dā, shahararru.

5 Ubangiji kuwa ya ga muguntar mutum ta ƙasaita a duniya, dukan zace-zacen tunanin zuciyarsa kuma mugunta ne kullayaumin.

6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya ɓata masa zuciya ƙwarai.

7 Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”

8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9 Waɗannan su ne zuriyar Nuhu. Nuhu adali ne, salihi ne kuma a cikin zamaninsa. Nuhu ya yi tafiya tare da Allah.

10 Nuhu kuwa ya haifi ‘ya’ya uku, Shem, da Ham, da Yafet.

11 Amma dukan sauran mutane mugaye ne a gaban Allah, muguntarsu kuwa ta bazu ko’ina.

12 Allah ya dubi duniya, ga shi kuwa ta ɓaci, gama dukan mutane sun lalatar da tafarkunsu a cikin duniya.

Nuhu ya Sassaƙa Jirgi

13 Allah ya ce wa Nuhu, “Na riga na yi niyyar hallaka dukan talikai, gama duniya tana cike da ayyukansu na zunubi.

14 Ka sassaƙa wa kanka jirgi na itacen gofer, ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka dalaye cikinsa da bayansa da ƙaro.

15 Ga yadda za ka sassaƙa shi, tsawon jirgin ƙafa ɗari huɗu da hamsin, faɗinsa ƙafa saba’in da biyar, tsayinsa ƙafa arba’in da biyar.

16 Ka yi wa jirgin rufe, ka bar inci goma sha takwas tsakanin rufin da gyaffansa. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.

17 Gama ga shi, zan kawo rigyawa bisa duniya, ta hallaka dukan mai numfashin rai da yake ƙarƙashin sama, dukan abin da yake a duniya zai mutu.

18 Amma ni zan kafa alkawari tsakanina da kai, za ka shiga cikin jirgin, kai da ‘ya’yanka, da matarka, da matan ‘ya’yanka tare da kai.

19 Daga kowane irin mai rai kuma za ka shigar da biyu biyu a cikin jirgin, domin su rayu tare da kai, amma su kasance namiji da ta mace.

20 Tsuntsaye bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kowane irin mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsa, biyu biyu na kowane iri za su shiga tare da kai, su rayu.

21 Ka ɗauki kuma kowane irin abinci da ake ci, ka tanada, zai kuwa zama abincinka da nasu.”

22 Nuhu ya yi dukan abin da Allah ya umarce shi.

Categories
FAR

FAR 7

Ruwan Tsufana

1 Sai Ubangiji ya ce wa Nuhu, “Ka shiga jirgin, kai da iyalinka duka, gama na ga a wannan zamani, kai adali ne a gare ni.

2 Daga cikin dabbobi masu tsarki ka ɗauki bakwai bakwai, namiji da ta mace, marasa tsarki kuwa namiji da ta mace,

3 da kuma tsuntsayen sararin sama bakwai bakwai, namiji da ta mace, domin a wanzar da irinsu a duniya duka.

4 Gama da sauran kwana bakwai kāna in sa a yi ruwa a duniya yini arba’in da dare arba’in. Dukan abu mai rai wanda na yi zan shafe shi daga duniya.”

5 Nuhu kuwa ya yi dukan abin da Ubangiji ya umarce shi.

6 Nuhu yana da shekara ɗari shida lokacin da Ruwan Tsufana ya kwararo bisa duniya.

7 Nuhu da ‘ya’yansa da matarsa, da matan ‘ya’yansa tare da shi suka shiga jirgi, domin su tsira daga Ruwan Tsufana.

8 Daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da na tsuntsaye, da na kowane mai rarrafe a ƙasa,

9 biyu biyu, namiji da mata, suka shiga jirgi tare da Nuhu, kamar yadda Allah ya umarci Nuhu.

10 Sai bayan kwana bakwai ruwayen suka kwararo bisa duniya.

11 A ranar sha bakwai ga wata na biyu, na shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu, a ran nan sai dukan maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe, tagogin sammai suka buɗe.

12 Ruwa yana ta kwararowa bisa duniya yini arba’in da dare arba’in.

13 A wannan rana Nuhu da ‘ya’yansa, Shem, da Ham, da Yafet, da matar Nuhu da matan ‘ya’yansa tare suka shiga jirgin,

14 su da kowace dabbar jeji bisa ga irinta, da dukan dabbobin gida bisa ga irinsu, da kowane mai rarrafe wanda yake rarrafe bisa ƙasa, bisa ga irinsa, da kowane tsuntsun gida da na jeji wanda yake numfashi.

15-16 Su waɗanda suka shiga, namiji ne da ta mace na kowane taliki, suka shiga jirgin kamar yadda Allah ya umarce shi. Sai Ubangiji ya kulle jirgi daga baya.

17 Aka yi ta kwararo ruwa bisa duniya har kwana arba’in, ruwayen kuwa suka ƙaru, har suka ɗaga jirgin sama, ya kuwa tashi can ƙoli birbishin duniya.

18 Ruwa ya bunƙasa ya ƙaru ƙwarai bisa duniya, jirgin kuwa ya yi ta yawo bisa fuskar ruwaye.

19 Ruwa kuwa ya bunƙasa ainun a bisa duniya, har ya rufe kawunan dukan duwatsu masu tsayi da yake ƙarƙashin sammai duka.

20 Ruwa ya bunƙasa bisa duwatsu ya yi musu zara da ƙafa ashirin da biyar.

21 Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum,

22 da kowane abin da yake bisa sandararriyar ƙasa wanda yake da numfashin rai cikin kafafen hancinsa ya mutu.

23 Ubangiji ya shafe kowane mai rai wanda yake bisa ƙasa, da mutum, da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, an shafe su daga duniya. Nuhu kaɗai aka bari, da waɗanda suke tare da shi cikin jirgi.

24 Ruwa kuma ya mamaye duniya har kwana ɗari da hamsin.

Categories
FAR

FAR 8

Ƙarshen Ruwan Tsufana

1 Allah kuwa ya tuna da Nuhu da dukan dabbobin gida da na jeji waɗanda suke cikin jirgi tare da shi. Allah ya sa iska ta hura bisa duniya, ruwaye suka janye.

2 Maɓuɓɓugan zurfafa da tagogin sammai suka rufe, aka dakatar da ruwa daga sammai,

3 ruwa ya yi ta janyewa daga duniya. Bayan kwana ɗari da hamsin sai ruwa ya ragu.

4 Ya zama kuwa a ran sha bakwai ga wata na bakwai, sai jirgin ya tafi ya tsaya bisa kan dutsen Ararat.

5 Ruwa ya yi ta raguwa har wata na goma. A ran ɗaya ga wata na goma, sai kawunan duwatsu suka ɓullo.

6 A ƙarshen kwana arba’in Nuhu ya buɗe tagar jirgin da ya yi,

7 sai ya saki hankaka. Hankaka ya yi ta kai da kawowa har lokacin da ruwan ya ƙafe a duniya.

8 Sai kuma ya aiki kurciya ta gani ko ruwa ya janye,

9 amma kurciyar ba ta sami inda za ta sauka ba, sai ta komo wurinsa cikin jirgi, gama har yanzu ruwa na rufe ƙasa duka. Sai ya miƙa hannunsa ya ɗauko ta ya shigar da ita cikin jirgi tare da shi.

10 Ya jira kuma har kwana bakwai, sai kuma ya sāke aiken kurciyar daga cikin jirgin.

11 Kurciyar kuwa ta komo wurinsa da maraice, ga shi kuwa, a bakinta sabon tohon zaitun wanda ta tsinko, domin haka Nuhu ya gane ruwa ya janye daga duniya.

12 Sai ya sāke dakatawa har kwana bakwai, ya kuma aiki kurciya, amma ba ta ƙara komowa wurinsa ba.

13 A rana ta fari ga wata na fari na shekara ta ɗari shida da ɗaya na Nuhu, ruwa ya ƙafe a duniya. Sai Nuhu ya buɗe murfin jirgin, ya duba, sai ga ƙasa busasshiya.

14 Ran ashirin da bakwai ga wata na biyu, duniya ta bushe.

15 Sa’an nan sai Allah ya ce wa Nuhu,

16 “Fito daga cikin jirgi, kai da matarka, da ‘ya’yanka da matan ‘ya’yanka tare da kai.

17 Ka fito da kowane abu mai rai tare da kai, dukan talikai, wato tsuntsaye, da dabbobi, da kowane abu mai rarrafen da yake rarrafe bisa ƙasa, domin su hayayyafa su kuma riɓaɓɓanya a duniya.”

18 Sai Nuhu ya fito, da ‘ya’yansa, da matarsa da matan ‘ya’yansa tare da shi,

19 da kowace irin dabba, da kowane mai rarrafe, da kowane irin tsuntsu, da kowane irin abin da yake motsi a bisa duniya, suka fito daga jirgi ɗaki ɗaki bisa ga irinsu.

Nuhu ya Miƙa Hadaya

20 Nuhu ya gina wa Ubangiji bagade, ya ɗiba daga cikin kowace irin dabba mai tsarki, da kowane tsuntsu mai tsarki, ya miƙa hadayu na ƙonawa a bisa bagaden.

21 Sa’ad da Ubangiji ya ji ƙanshi mai daɗi, sai ya ce, “Ba zan ƙara la’anta ƙasa sabili da mutum ba, ko da yake zace-zacen zuciyar mutum mugunta ne tun daga ƙuruciyarsa. Ba zan kuma ƙara hallaka kowane mai rai ba kamar yadda na yi a dā.

22 Muddin duniya tana nan, lokacin shuka da lokacin girbi, damuna da rani, yini da dare, ba za su daina ba.”

Categories
FAR

FAR 9

Allah ya Yi Alkawari da Nuhu

1 Allah kuwa ya sa wa Nuhu da ‘ya’yansa albarka, ya ce musu, “Ku yi ‘ya’ya ku hayayyafa, ku cika duniya.

2 Kowace dabba ta duniya, da kowane tsuntsu na sararin sama, da kowane mai rarrafe a ƙasa, da dukan kifaye na teku, za su riƙa jin tsoronku suna fargaba. An ba da su a hannunku.

3 Kowane abu mai motsi wanda yake da rai, zai zama abincinku. Daidai kamar yadda na ba ku ɗanyun ganyaye, na ba ku kome da kome.

4 Akwai abu ɗaya da ba za ku ci ba, shi ne naman da jininsa yake cikinsa, wato mushe.

5 Idan wani ya kashe ka zan hukunta shi da mutuwa. Zan kashe dabbar da za ta kashe ka, zan hukunta duk wanda ya kashe mutum ɗan’uwansa.

6 “Duk wanda ya kashe mutum, ta hannun mutum za a kashe shi, gama Allah ya yi mutum cikin siffarsa.

7 Amma ku, ku yi ‘ya’ya ku hayayyafa, ku riɓaɓɓanya a duniya ku yawaita a cikinta.”

8 Allah kuwa ya ce wa Nuhu da ‘ya’yansa.

9 “Ga shi, na kafa alkawari tsakanina da ku da zuriyarku a bayanku,

10 da kowane mai rai da yake tare da ku, da tsuntsaye, da dabbobin gida da na jeji, duk dai iyakar abin da ya fita daga jirgin, kowane mai rai na duniya.

11 Na kafa alkawarina da ku. Daɗai ba za a ƙara hallaka talikai duka da ruwa ba, ba kuma za a ƙara yin Ruwan Tsufana da zai hallaka duniya ba.”

12 Allah ya ce, “Wannan ita ce alamar alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da yake tare da ku, har dukan zamanai masu zuwa,

13 na sa bakana cikin girgije, ya zama alamar alkawari tsakanina da duniya.

14 Sa’ad da na kawo gizagizai bisa duniya, aka ga bakan a cikin gizagizai,

15 zan tuna da alkawarin da yake tsakanina da ku, da kowane mai rai da dukan talikai. Ruwa kuma ba zai ƙara yin rigyawar da za ta hallaka talikai duka ba.

16 Sa’ad da bakan yake cikin girgije zan dube shi, in tuna da madawwamin alkawari tsakanin Allah da kowane mai rai da dukan talikan da suke bisa duniya.”

17 Allah ya ce wa Nuhu, “Wannan ita ce alamar alkawari wanda na kafa tsakanina da dukan talikan da suke bisa duniya.”

Nuhu da ‘Ya’yansa Maza

18 ‘Ya’yan Nuhu waɗanda suka fito daga jirgi su ne Shem, da Ham, da Yafet. Ham shi ne mahaifin Kan’ana.

19 Su uku ɗin nan su ne ‘ya’yan Nuhu, daga gare su duniya za ta cika da mutane.

20 Nuhu shi ya fara noma, ya yi gonar inabi.

21 Ya sha daga cikin ruwan inabin ya kuwa bugu, ya kwanta tsirara a cikin alfarwarsa.

22 Sai Ham, mahaifin Kan’ana, ya ga tsiraicin mahaifinsa, ya faɗa wa ‘yan’uwansa biyu waɗanda suke waje.

23 Sai Shem da Yafet suka ɗauki riga, suka ɗibiya bisa kafaɗunsu, suka yi tafiya da baya da baya suka rufa tsiraicin mahaifinsu, suka juya fuskokinsu, ba su kuwa ga tsiraicin mahaifinsu ba.

24 Sa’ad da ruwan inabin ya sau Nuhu, ya san abin da ƙaramin ɗansa ya yi masa.

25 Sai ya ce, “La’ananne ne Kan’ana, bawan bayi zai zama ga ‘yan’uwansa.”

26 Ya kuma ce, “Bari Ubangiji Allahna, ya sa wa Shem albarka, Kan’ana kuwa ya bauta masa.

27 Allah ya sa Yafet ya yawaita, ya sa ya zauna a alfarwan Shem, Kan’ana kuwa ya bauta masa.”

28 Bayan Ruwan Tsufana, Nuhu ya yi shekara ɗari uku da hamsin.

29 Shekarun Nuhu duka ɗari tara da hamsin ne, ya rasu.

Categories
FAR

FAR 10

Zuriyar ‘Ya’yan Nuhu, Maza

1 Waɗannan su ne zuriyar ‘ya’yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu ‘ya’ya.

2 ‘Ya’yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras.

3 ‘Ya’yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma.

4 ‘Ya’yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim.

5 Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu.

6 ‘Ya’yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan’ana.

7 ‘Ya’yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra’ama, da Sabteka. ‘Ya’yan Ra’ama kuwa Sheba da Dedan.

8 Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya.

9 Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.”

10 Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke.

11 Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala,

12 da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato babban birni.

13 Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa,

14 da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.

15 Kan’ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het,

16 shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa,

17 da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa,

18 da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan’aniyawa suka yaɗu.

19 Yankin ƙasar Kan’aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha.

20 Waɗannan su ne ‘ya’yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu.

21 An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, ‘ya’ya, shi ne kakan ‘ya’yan Eber duka.

22 ‘Ya’yan Shem su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram.

23 ‘Ya’yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek.

24 Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber.

25 An haifa wa Eber ‘ya’ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan’uwansa kuwa Yokatan.

26 Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera,

27 da Adoniram, da Uzal, da Dikla,

28 da Ebal, da Abimayel, da Sheba,

29 da Ofir, da Hawila da Yobab, dukan waɗannan ‘ya’yan Yokatan ne.

30 Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas.

31 Waɗannan su ne ‘ya’yan Shem bisa ga iyalansu, da harsunansu, da ƙasashensu, da kabilansu.

32 Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al’ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.